logo

HAUSA

Yin kasuwanci tare da kasar Sin shi ne zabin karin kamfanonin kasashe

2022-10-12 20:17:43 CMG Hausa

A yayin taron kolin injinya na Berlin da aka gudanar a kwanan nan, batun kiyaye huldar kasuwanci da kasar Sin ya kasance babban batu da aka tattauna a taro. Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ya sake bayyanawa karara cewa, yana goyon bayan dunkulewar duniya, inda ya yi nuni da cewa, ware kai daga wata kasa, batu ne da ko kadan bai dace ba. Ya kuma jaddada cewa, ya zama tilas a yi kasuwanci da kasashe da dama, ciki har da kasar Sin.

Kwamishinan kasuwanci na kungiyar Tarayyar Turai Valdis Dombrovski, ya bayyana a fili cewa, kauracewa kasar Sin ba zabi ba ne ga kamfanonin EU, domin kasar Sin babbar kasuwa ce dake ci gaba da samar da kayayyaki. A yayin da wasu kasashe ke ba da shawarar ware kai da karuwar barazanar koma bayan tattalin arzikin duniya, ya kamata a saurari muryar wadannan jami'an Turai da idon basira. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)