logo

HAUSA

Bala’in ambaliyar ruwa a daminar bana a Nijeriya ya haddasa mutuwar mutane fiye da 500

2022-10-12 13:38:09 CMG Hausa

 

Sakataren ma’aikatar harkokin jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban al’umma a Najeriya Nasir Sani Gwarzo, ya ce bala’in ambaliyar ruwa dake faruwa a yankuna daban daban na Nijeriya, ya haddasa mutuwar mutane fiye da 500, tare da jikkata mutum 1,546.

Sani Gwarzo ya bayyana hakan ne a jiya Talata a birnin Abuja, fadar mulkin kasar yayin taron ’yan jarida da aka gudanar, inda ya ce tun daga farkon daminar bana zuwa yanzu, babban birnin tarayyar Nijeriya da jihohi 31, na fama da ambaliyar ruwa iri iri, waadda ta shafi mutane fiye da miliyan 1.4, kuma mutane fiye da dubu 790 sun rasa gidajensu.

Sani Gwarzo ya ce, bala’in ambaliyar ruwa ya haddasa lalacewar gidaje kusan dubu 90 a fadin kasar, kuma ta lalata gonaki da fadinsu ya kai hekta fiye da dubu 140. Ya ce babban birnin tarayyar Nijeriya da gwamnatocin jihohin kasar, sun riga sun dauki matakan gaggawa, sun ba da tallafi ga jama’a da bala’in ya shafa, kuma suna kokarin rage tasirin bala'in. (Safiyah Ma)