logo

HAUSA

An shirya darasin kimiyya na farko daga tashar binciken sararin samaniya ta Sin

2022-10-12 20:00:11 CMG Hausa

A yau ne, kasar Sin ta watsa darasi na farko game da kimiyya da aka shirya daga dakin gwaje-gwaje na Wentian na tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin.

Wannan shi ne aji na farko da 'yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 wato Chen Dong da Liu Yang da Cai Xuzhe suka gabatar, wadanda aka harba su zuwa tashar binciken sararin samaniyar kasar a ranar 5 ga watan Yuni, don gudanar da aiki na tsawon watanni 6, kuma irinsa na 3 da ‘yan sama jannatin na kasar Sin suka gabatar daga sararin samaniya.(Ibrahim)