logo

HAUSA

Sin ta yi na’am da bayani mai kyau da Scholz ya yi game da adawar mayar da wasu saniyar ware

2022-10-12 18:57:26 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin yau Laraba, ta yi marhabin da “bayani mai kyau” da shugaban gwamnatin Jamus Plaf Scholz da sauran shugabannin kasashen Turai suka yi kan nuna rashin amincewa da yankurin ware kai ko mayar da wasu kasashe saniyar ware daga tsarin tattalin arzikin duniya.

A yayin taron kolin injiniya karo na 13 na kasar Jamus da ya gudana a Berlin jiya Talata, Scholz ya sake nanata muhimmancin dunkulewar duniya wajen samun ci gaba tare da nuna adawa da ra’ayin ware kai daga kasashe ciki har da kasar Sin. (Ibrahim)