logo

HAUSA

Peng Liyuan ta aike da sakon taya murna ga taron karrama wadanda suka yi fice a fannin tallafawa ilimin mata

2022-10-12 11:14:47 CMG Hausa

Mai dakin shugaban kasar Sin Peng Liyuan, ta aike da sakon taya murnar bikin karrama wadanda suka yi fice, a fannin tallafawa ilimin yara mata da mata na bana, wanda ya gudana a jiya Talata a birnin Paris na kasar Faransa, karkashin jagorancin hukumar raya ilimi kimiyya da al’adu ta MDD UNESCO.

Cikin wasikar, Peng Liyuan, wadda kuma ita ce jakadiyar musamman ta asusun UNESCO, mai lura da manufar ingiza ilimin yara mata da mata, ta ce alfanun samar da ilimi ga wannan rukuni na al’umma ya wuce batun bunkasa rayuwar mata kadai, duba da cewa, hakan muhimmin jigo ne na ingiza ci gaba mai dorewa ga daukacin al’ummun duniya.

Peng Liyuan, ta ce yayin taron baya bayan nan na MDD game da kyautata tsarin samar da ilimi, an jaddada muhimmancin ilimi wajen inigiza daidaiton jinsi, inda aka yi kira da a karfafa rayuwar mata, ta hanyar samar musu da ingantacen ilimi.

Peng ta kara da cewa, har kullum kasar Sin na dora muhimmancin gaske, ga batun raya ilimin yara mata da mata, yayin da kuma ake ci gaba da inganta damar su ta shiga a dama da su, a harkokin raya tattalin arziki, da ci gaban zamantakewa da sauran su. (Saminu Alhassan)