logo

HAUSA

Dalilan Da Suka Sa Kauyukan Sin Samun Ci Gaba

2022-10-11 20:33:35 CMG Hausa

Sharhi daga Bello Wang

Wasu abokaina ‘yan Najeriya, wadanda suka taba zama a kasar Sin, su kan ambaci yadda zaman rayuwa a cikin biranen Sin ya burge su, yayin da muke hira. Sai dai na kan tunatar da su cewa, ba abun mamaki ba ne, ganin irin saurin ci gaba da aka samu a kauyukan kasar Sin.

Kauyena yana lardin Anhui dake gabashin kasar Sin, wani wuri ne dake cikin duwatsu. Yayin da nake karami, ba na son komawa kauyen tare da iyayena, saboda hanyar ba ta da kyau: a kan kwashe sa’o’i 10 a cikin jirgin kasa, sa’an nan a ci gaba da hawa tarakta har tsawon awa daya. Ban da wannan kuma, bayan gidan da mutanen kauyen suke amfani da shi ba shi tsabta, hakan yana tsorata ni.

Sai dai zuwa yanzu, kauyen ba kamar yadda yake a baya ba. Jirgin kasa mai saurin gudu ya samar da sauki sosai ga mutanen da suke neman komawa kauyen. Kana mutanen wurin sun gina manyan benaye, ga kuma muhalli mai tsabta da kayatarwa. Ban da haka kuma sun fara yin amfani da dakunan dake cikin gidajensu wajen karbar baki masu yawon shakatawa.

To, me ya sa ake samun ci gaba sosai a kauyukan kasar Sin, cikin gomman shekaru da suka wuce?

Dalili na farko, a ganina, shi ne niyyar gwamnati ta raya kayuka, da yadda take kokarin aiwatar da niyyar.

Babbar manufar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin dake kan karagar mulki a kasar, ita ce kokarin kyautata zaman rayuwar jama’a. Saboda haka gwamnatin kasar ba za ta taba barin ragowar sassan kasar, ko kuma wasu mutane a baya ba, yayin da take kokarin raya tattalin arzikin kasar. Hakan ya sa gwamnati ta fito da dimbin manufofi wajen raya kauyuka, da kyautata zaman rayuwar manoma. Misali taimakawa kauyuka wajen janyo jari, da samarwa manoma fasahohin zamani na aikin gona, da samar da rance don raya aikin yawon shakatawa a yankin karkara, da dai sauransu.

Dalili na biyu, shi ne yadda wasu matasan kauyuka suka komawa gida, bayan da suka samu ilimi, don taimakawa wajen raya kauyukansu. A cikin kauyukan da na ziyarta a shekarun baya, na kan ga wasu matasan da suka kammala karatun jami’a a cikin manyan birane, inda suka shafe wasu shekaru suna aiki a can, daga bisani sun koma kauyukansu, sun fara aiki a matsayin jami’ai. Yadda aka wayar musu da kai, ya samar musu da damammakin raya wasu sana’o’i da suka dace da yanayin kauyukan, kana sun fahimci muhimmancin yin amfani da manufofin da gwamnati ta tsara na raya yankunan karkara.

Ban da wannan kuma, dalili na uku shi ne al’adun Sinawa na jure wahalhalu da kokarin aiki. A kauyukan da na je, na ga wasu tsoffi da yawa da suke gudanar da ayyuka daban daban, misali sayar da kaya, ko kuma nuna fasahohin hannu, har ma wasunsu na tuka manyan motocin tsabtace muhalli. Haka ma dattawa na kokarin aiki, balle ma matasa. Sinawa suna daukar kokarin aiki a matsayin wata muhimmiyar da’a. Kana nagartattun manufofin gwamnati su ma sun sa mutanen kasar ke da wani tunani na kokarin aiki da samar da hidimomi, don kyautata rayuwarsu, gami da ba da gudunmowa ga ci gaban kasa.

A cikin kauyukan kasar Sin, ana iya ganin yadda mazauna suke da imanin cewar, za su kara jin dadin zaman rayuwarsu a nan gaba. Wannan imani ya tabbatar da cewa, ba za a taba daina kokarin raya kauyukan kasar, da kyautata zaman rayuwar jama’ar wuraren ba. (Bello Wang)