logo

HAUSA

Sin: Matakin da Amurka ta dauka babakere ne ta fannin kimiyya

2022-10-11 11:42:03 CMG Hausa

A game da yadda kasar Amurka ta tsaurara matakan kayyade fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin, ta bangarorin hada na'urorin latironi na “semi conductor”, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayyana cewa, wannan babakere ne na zahiri ta fannin kimiyya.

A cewar kakakin, hakan ya saba wa manufar hadin gwiwar kasashen biyu, har ma ya haifar da tsaiko ga mu’amalar dake tsakanin kamfanonin kasashen biyu, baya ga kuma yadda hakan ya keta dokokin kasuwanci da ma tsarin tattalin arziki da ciniki na duniya, tare da haifar da barazana ga tsarin samar da kayayyaki na duniya, don haka, kasar Sin ta bayyana rashin amincewarta da kakkausar murya.

Kakakin ta kara da cewa, kamata ya yi Amurka ta dakatar da wannan mataki na kuskure nan da nan, kuma ta yi wa kamfanonin kasar Sin da na sauran kasashe adalci. Kasar Sin ta kuma yi kira ga sassan kasa da kasa, da su inganta hadin gwiwa, don kafa tsarin samar da kayayyaki mai inganci, wanda zai amfani kasa da kasa. (Lubabatu Lei)