logo

HAUSA

Tawagar kasar Sin ta halarci babban taro na 16 na kwamitin ICG

2022-10-11 14:21:56 CMG Hausa

An bude babban taro karo na 16 na kwamitin ICG, wato kwamitin hadin-gwiwar kasa da kasa mai lura da ayyukan tauraron dan adam, a ranar 9 ga watan nan a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa, taron da zai gudana har zuwa ranar 14 ga wata. A yayin taron, wakilan bangarori daban-daban za su yi musanyar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi amfani da taurarin dan Adam a sararin samaniya.

Wani kwararre daga kasar Sin ya gabatar da jawabi game da sabon ci gaban da aka samu, wajen amfani da tsarin shawagin taurarin dan Adam da ake kira Beidou, a fannonin da suka shafi tallata amfaninsa, da hadin-gwiwar kasa da kasa.

A nata bangaren, mataimakiyar darektar cibiyar samar da hidimomin lokuta ta kasa, dake karkashin kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, wadda kuma ita ce mataimakiyar darektar cibiyar kula da ayyukan hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin amfani da tsarin Beidou Lu Xiaochun, tana ganin cewa, halartar tsarin Beidou wannan taro na kwamitin ICG na da babbar ma’ana, tana mai cewa:

“Kwamitin ICG na da matukar muhimmanci, wanda ya yi kama da ‘Majalisar Dinkin Duniya’ a fannin shawagin taurarin dan Adam. Tsarin Beidou na kasar Sin yana fitar da shawarwarin kasar gami da muryoyinta, haka kuma, muna da yakinin cewa, Beidou wani tsarin shawagin taurarin dan Adam ne mai inganci a duk duniya.”

Wakilai daga sauran kasashe, ciki har da na Pakistan, sun bayyana cewa, tsarin Beidou na kasar Sin ya fi taka rawa, idan aka kwatanta da sauran wasu tsare-tsaren shawagin taurarin dan Adam, kana, tsarin Beidou yana kokarin samar da goyon-baya ga kasashe masu tasowa, wadanda ke bunkasa fasahohin amfani da taurarin dan Adam, al’amarin da ya bayar da babbar gudummawa ga ci gaban duniya baki daya. (Murtala Zhang)