logo

HAUSA

Wang Chunxing dattijo mai aikin sa kai domin kauna da kare rayuka

2022-10-10 10:34:41 CRI

Tun kafin rana ta daga sama, dattijo Wang Chunxing mai shekaru 66 a duniya, kan fito yana tattaki sannu a hankali zuwa cikin ruwa, inda yake fara linkaya. Da shigar sa ruwa cikin ‘yan mintuna ya yi nisan mitoci.

A yayin gasar wasanni 3 a hade, wani bangare na gasar Olympic dake hada linkaya, da tseren keke, da tafiya mai nisa, akan bukaci yin linkaya ta kilomita 1.5 ne. Amma fa Wang na yin linkayar kilomita 2 a sa’i daya, kuma yana yin linkaya ne kusan kullum.

Manhajar sa ta auna yanayin lafiyar jiki, ta nuna ya yi linkaya sau 30 a watan Yuni, da sau 29 a watan Yuli, da sau 19 a Agusta, har ma a ranekun lokacin hunturu masu sanyin gaske, Wang na yin linkaya mai yawa a wasu kwanaki. Wang ya taba yin saurin linkaya na kilomita 1 a mintuna 25, saurin da ko da yake bai kai na kwararrun ‘yan linkaya ba, amma yana kan gaba a ajin masu linkaya na gama-gari. Shekaru 3 da suka gabata, ‘yan sandan Nanchang sun gudanar da gasar linkaya ta kilomita 5 a kogin Ganjiang, inda suka gayyaci kungiyar linkaya ta Wang. Ba tare da sun mayar da hankali ba, sai matasan da suka shiga gasar suka ga har Wang ya wuce kowa, ya kai karshen wurin da aka tsara kammala linkayar.

Wang yana aiki ne a mahakar Kwal lokacin yana matashi; ya kuma halarci kwaleji, kana daga baya ya yi aiki a sashen masu binciken albarkatun karkashin kasa. Wang ya ce abubuwan da ya kan yi a kullum sun hada da ko dai hawa tsauni, ko tafiya da kafa, kuma wata kila ma yana tafiya fiye da kima, kana linkaya ta zame masa abun da ya saba da shi a rayuwarsa.

Sakamakon dorewa da motsa jiki, bugun zuciyarsa ya ci gaba da kasancewa kan kimanin bugu 60 a duk minti, kana sakamakon gwajin lafiyarsa, ya nuna ba shi da wani ciwo mai nasaba da hawan jini, ko yawan kitse a cikin jini, ko yawan sukari a cikin jini.

Shekaru 5 da suka gabata, Wang ya yi ritaya, ya kuma koma garin Nanchang. Ya sayi gida a kusa da dandalin Changtian, ta yadda tsallaka titi kawai zai yi zuwa kogin dake daura da gidan sa. A can ne kuma ya hadu da abokan linkayarsa.

Ya ce "Da farko akwai kimanin mutane 20; mafi yawan su ‘yan shekaru sama da 60 ne, wadanda sun jima suna linkaya ta kimanin a kalla shekaru 10. Sun fara linkaya tun suna da kuruciya, suka kuma ci gaba da yi har zuwa yanzu. Yanayin wannan kogi mai fadi, na yiwa masu linkaya dadi, to sai dai kuma a wasu lokuta yana tattare da hadari. Idan na ga wani a cikin hali mai hadari yayin da nake linkaya, tabbas zan yi kokarin ceton sa. Sai dai fa ni ba kwararre ba ne"

Wang ya kara da ce, shi da abokan linkayarsa, sun yi hadin gwiwa da kungiyar ba da agajin jin kai ta “Red Cross” reshen Jiangxi, inda a ko da yaushe suke aikin kare mutane daga nutsewa a ruwa.

Ba abu ne mai sauki ga Wang da abokan linkayarsa, su sauya daga masu sha’awar linkaya zuwa masu ceton mutane daga ruwa ba. Amma duk da haka, da taimakon tawagar ta Red Cross, sun koyi yadda ake farfado da numfashin wanda ya fada ruwa, da yadda ake farfado da huhun wanda ya kusa nutsewa a ruwa, da sauran ayyukan ba da taimakon farko.

Tun daga karfe 6:00 na safiya har zuwa 7:30 na almuru, wanda shi ne lokacin da aka fi samun masu zuwa linkaya kogin, Wang da sauran ‘yan tawagar na aiki bi da bi, wajen kare rayukan mutane ta hanyar ceto masu nutsewa a ruwa.

Sabanin da sanyin safiya, a wannan karo, Wang zai sanya rigar kariyar jiki da igiyar jefawa cikin ruwa, yana rike da sandar kamun kifi, da sauran kayayyakin ceton mutane a hannu guda, a daya hannun kuma yana rike da na’urar amsa kuwa. Yana kai-komo a tsawon kilomita 5 ta bakin kogin, har lokacin da ‘yan yawon bude ido za su bar wuri.

Wang ya ce "Ina gargadin matasa, da mutanen dake son yin linkaya ba tare da kariya ba. Wata rana wani yaro ya bace a cikin ruwa, bayan da ya yi linkaya ta ‘yan mitoci, nan da nan na yi nutso cikin kogin na tsamo shi, daga baya na gane cewa wannan ne karo na 2 da yaron ya fara gwada yin linkaya".

Bayan dan lokaci, kwazon tawagar su Wang ya bazu a ko ina. A wasu lokutan masu wucewa za su kira tawagar Wang kai tsaye, da zarar sun hangi wani a cikin hadarin nutsewa. Wang ya ce yayin hutun lokacin zafi an fi samun yawaitar hadurran nutsewa a ruwa, a wannan lokaci, tawagar su na gargadin kusan matasa 30 zuwa 50 a kullum, da kada su yi linkaya ba tare da kulawar manya ba, kuma adadin kan yi matukar yawa a ranakun karshen mako.

Cikin kusan shekaru 6, Wang da abokan aikin sa sun ceto sama da mutane 30 daga ruwa. Ya ce "Duk mutum guda bangare ne na wani iyali, don haka kamar mun ceto iyalai sama da 30 ne".

Wang na da wasu burika, da suka hada da ci gaba da aiki tare da abokan linkayarsa kafin ya cika shekaru 70, kana yana fatan ci gaba da yin linkaya a kullum bayan ya haura shekaru 80.