logo

HAUSA

Mutane 76 sun mutu sakamakon nutsewar kwale-kwale a kudancin kasar Najeriya

2022-10-10 10:19:39 CMG HAUSA

 

Fadar shugaban kasar Najeriya ta sanar a jiya Lahadi cewa, mutane 76 sun mutu, samakakon nutsewar wani kwale-kwale a jihar Anambra dake kudancin kasar.

Sanarwar ta ce, wani kwale kwale dauke da mutane 85 ya gamu da hadari saboda ambaliyar ruwa a wani kogin dake jihar Anambra, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 76. Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan mamatan, tare da ba da umurni ga hukumar agajin gaggawa da ta yi iyakacin kokarin gano wadanda suka bace.

Kafar yada labarai ta jihar ta ruwaito wani jami’i mai kula da ayyukan agaji a jihar na cewa, wurin da aka gamu da hadarin na fama da karuwar ruwan kogin saboda ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a cikin jerin kwanakin da suka gabata. Yana mai cewa, kwale-kwalen ya gamu da hadarin ne yayin da ake kokarin tsugunar da mutanen dake fama da bala’in. (Amina Xu)