logo

HAUSA

An samu hadarin kifewar jirgin ruwa a kudancin Najeriya

2022-10-09 15:57:40 CMG Hausa

Jiya Asabar 8 ga wata, hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Anambra dake kudancin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, an samu hadarin kifewar jirgin ruwa a ranar 7 ga wata, inda ake fargabar mutane sama da 70 sun rasa rayukansu.

Jami’in hukumar ya bayyana cewa, a safiyar ranar, wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji 85 ya kifa, sakamakon ambaliyar ruwa, inda aka yi nasarar ceto mutane 9 kacal daga hadarin.

A bana ruwan saman da aka rika shekawa a kasar, ya dara na bara, rahotannin sun nuna cewa, ya zuwa tsakiyar watan Satumban da ya gabata, sama da mutane 300 ne suka rasu a kasar sakamakon ambaliyar ruwa, bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, kana mutane dubu 100 sun rasa muhallansu. (Jamila)