logo

HAUSA

Rahoto: Kasar Sin ta kara saurin inganta bangaren makamashi ba tare da gurbata muhalli ba cikin shekaru goma da suka gabata

2022-10-09 16:08:50 CMG Hausa

Wani rahoto da hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar kan sauyin da aka samu a bangaren makamashin kasar ba tare da gurbta muhalli ba, da karancin fitar da iskar Carbon mai gurbata muhallin duniyarmu a cikin shekaru goma da suka gabata ya nuna cewa, yawan wutar lantarkin da kasar ke samarwa, ya karu da fiye da kashi 70 cikin 100, idan aka kwatanta da shekarar 2012, ciki har da karuwar na’urorin samar da makamashi mai tsafta da kashi 700 cikin 100.

Rahoton ya bayyana cewa, a cikin shekarar 2021, kasar Sin ta samar da wutar lantarkin da yawansa ya kai Kwh triliyan 8.5, wanda ya karu da kashi 71.1 cikin 100, idan aka kwatanta da shekara 2012, inda aka samu matsakaicin karuwar kasha 6.1 cikin 100 a duk shekara.

Idan aka kwatanta da shekarar 2012, adadin wutar lantarkin da ake samu daga karfin iska, da hasken rana da sauran sabbin hanyoyin samar da makamashi a shekarar 2021, ya ninka sau 6.8, inda aka samu karuwar kashi 25.7 a duk shekara.  Sabbin hanyoyin samar da makamashi, ya kai kashi 11.5 cikin 100 na yawan wutar lantarkin da ake sawarwa, wanda ya karu da kaso 9 kan na shekarar 2012.

A shekarar 2021 kuwa, karfin samar da wutar lantarki da ba na burbushin halittu ba, ya zarce na makamashin kwal a karon farko, wanda ya kai kw biliyan 1.12, kana ya kai kaso 47 cikin 100 na yawan karfin samar da wutar lantarki a duk fadin kasar.

Karfin samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa da iska da hasken rana a kasar Sin, kowanne ya dara kw miliyan 300. (Ibrahim)