logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi cikakken bayani kan sakamakon da jihar Xinjiang ta samu wajen kare hakkin bil Adam

2022-10-09 15:43:38 CMG Hausa

A yayin taro karo na 51 da hukumar kare hakkin bil Adam ta MDD ta kira kwanan baya, wakilin kasar Sin ya yi cikakken bayani kan babban sakamakon da jihar Xinjiang ta samu a wannan bangaren, inda ya yi nuni da cewa, jihar Xinjiang ta kasar Sin tana daukar batutuwan da suka shafi jin dadin rayuwar jama’a a matsayin hakkin bil Adam mafi muhimmanci bisa ka’idar martaba da tabbatar da hakkin bil Adam kamar yadda kundin dokokin kasar suka tanada, kuma ta ciyar da sha’anin kare hakkin bil Adam gaba ta hanyar daukar matakan kyautata rayuwar al’ummar jihar. An lura cewa, a jihar ta Xinjiang, duk da cewa, akwai bambancin adadi tsakanin kabilun jihar, da yanayi na tarihi, da matsayin samun ci gaba, da kuma al’adu, amma al’ummu ‘yan kabilu daban daban dake jihar, suna zaman jituwa ne bisa matsayi na daidai wa daida, kuma suna tafiyar da harkokin kasa da jihar tare, da ma jin dadin rayuwarsu tare yadda ya kamata. (Jamila)