logo

HAUSA

Shin Gwamnatin Birtaniya Ta Saurari Kiran Kungiyar OAS Kan Tsibiran Malvinas

2022-10-08 20:40:00 CMG Hausa

A yayin babban taro karo na 52, na kungiyar kasashen yankunan Amurka ko OAS a takaice, da suka hada da Latin Amurka da Amurka, wanda aka rufe a ranar 7 ga wata, wakilai mahalarta taron, sun zartas da kudurin kiyaye halastaccen ikon kasar Argentina kan tsibiran Malvinas, sun kuma yi kira da a daidaita sabanin ta hanyar shawarwari cikin ruwan sanyi.

Wannan ba shi ne karon farko da kungiyar OAS ta yi irin wannan kira bisa gaskiyar lamarin ba, kuma hakan ya bayyana ra’ayoyin bai daya na kasar Amurka da kasashen Latin Amurka, na neman kawar da illolin mulkin mallaka. Kamar yadda babban sakataren kungiyar ta OAS Luis Leonardo Almagro Lemes, ya furta cewa, kasancewar kasar Birtaniya kan wadannan tsibirai, lallai ba za a yarda da shi ba.

Haka zalika, a yayin taro karo na 51, na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD da aka rufe a kwanan baya, mahalarta taron sun bukaci Birtaniya, da sauran kasashen yammacin duniya, da su yi la’akari da laifin mulkin mallaka, su kuma gyara kuskuren su. Amma a nasu bangare ‘yan siyasar Birtaniya, sun yi shelar cewa, an riga an sa aya ga al’amura masu nasaba da hakan.

Ko shakka babu, bai kamata Birtaniya ta kau da kai daga kiran kasashen duniya bisa adalci ba. Wajibi ne ta waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ta gyara kuskuren ta, ta gaggauta mai da tsibiran Malvinas hannun Argentina. Tun tuni an sa aya ga mulkin mallaka, inda a halin yanzu ake raya hulda tsakanin kasa da kasa bisa demokuradiyya. (Tasallah Yuan)