logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya gabatarwa majalissar dokoki kasafin kudi na dalar Amurka biliyan 47

2022-10-08 15:59:38 CMG Hausa

 

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya gabatarwa zaman hadakar majalissun dokokin kasar daftarin kasafin kudin shekarar 2023, wanda ya kai naira tiriliyan 20.51, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 47.

Da yake gabatar da kasafin a jiya Juma’a, ya ce kasafin kudin ya dara na shekarar 2022, mai kunshe da naira tiriliyan 17.32, kuma kasafin na shekara mai zuwa zai mai da hankali ga tabbatar da kashe kudade bisa tsari, da yanayi mafi dacewa na mika mulki ga sabuwar gwamnati, a gabar da kasar ke tunkarar babban zabe, da mika mulki ga sabuwar gwamnatin da za ta kama aiki a shekarar badi.

An dai dora kasafin kudin na badi ne, kan hasashen hako danyen man da zai kai ganga miliyan 1.69 a ko wace rana, da hasashen sayar da danyen man kan dalar Amurka 70 ko wace ganga, yayin da ake hasashen karuwar ma’aunin GDPn kasar zuwa kaso 3.75 bisa dari, da kuma mizanin hauhawar farashin kayayyaki da zai kai kaso 17.16 bisa dari a shekarar ta 2023.

Shugaba Buhari, ya ce bisa kiyasi, gwamnatin Najeriya za ta tattara jimillar harajin da zai kai naira tiriliyan 16.87 a shekarar 2023. Ya ce "A wannan gaba da muke kokarin bunkasa tattalin arzikin kasa, ya zama wajibi mu mai da hankali ga kyautata amfani da ‘yan kudaden da muke samu. Muna daukar muhimman matakai da suka hada da gaggauta aiwatar da karin matakai, na rage tsadar gudanar da gwamnati, da kawo karshen biyan kudaden tallafin mai a shekarar 2023 dake tafe, kamar dai yadda tuni muka bayyana."  (Saminu Alhassan)