logo

HAUSA

Za a kaddamar da cibiyar watsa labaru ta taron wakilan JKS karo na 20 a ranar 12 ga watan Oktoba

2022-10-08 16:28:20 CMG Hausa

Za a kaddamar da cibiyar watsa labaru ta babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta Sin wato JKS karo na 20, a ranar Larabar makon gobe wato 12 ga watan Oktoban nan, tare da karbar ‘yan jarida a hukumance. An kafa sashen karbar ‘yan jarida, ta cibiyar, a otel din Nikko New Century dake nan birnin Beijing.

Cibiyar watsa labaru ta taron, za ta samar da hidima ga ‘yan jarida daga yankin Hong Kong, da na Macau, da na Taiwan, da kuma na kasashen waje, da za su watsa labaru game da taron, a fannonin samar musu takardun iznin watsa labaru, da karbar rokon watsa labarun, kana cibiyar za ta gudanar da taron manema labaru, da kuma shiryawa ‘yan jaridar da su shiga taron damar watsa labaru.

Za a kaddamar da shafin internet na cibiyar, wato http://20th.cpcnews.cn, da kuma sauran shafunan dandalin internet, a ranar 10 ga wannan wata a hukunce, a lokacin za a ba da labarai, da sanarwa game da taron, da kuma taron manema labaru kai tsaye. Kana an tanadi reshen musamman na shafin cibiyar, don samar da hidima ga ‘yan jarida a ciki da wajen kasar Sin, da suka yi rajistar watsa labaru game da taron. (Zainab)