logo

HAUSA

Kwamitin tsaron MDD ya nuna damuwa game da juyin mulki a Burkina Faso

2022-10-08 17:12:33 CMG Hausa

Kwamitin tsaron MDD, ya nuna matukar damuwa game da juyin mulkin da ya wakana a kasar Burkina Faso, a ranar 30 ga watan jiya, wanda ya hambarar da gwamnatin shugaba Paul-Henri Sandaogo Damiba. Kwamitin tsaron ya ce, juyin mulkin abun damuwa ne, duba da matsanancin yanayin kalubalen da yankin Sahel ke ciki a yanzu.

Mambobin kwamitin cikin wata sanarwa, sun ce juyin mulkin da ya biyo makamancin sa, da ya wakana watanni 8 kacal da suka wuce abun takaici ne, zai kuma yi kafar ungulu ga yanayin daidaito da ake fatan samu, don haka suka yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki a rikicin kasar dake yammacin Afirka, da su warware sabanin su ta hanyar tattaunawa.

A daya hannun, mambobin kwamitin na tsaro, sun yi maraba da matakin kungiyar ECOWAS, na shawo kan tashin hankali, da wawashe dukiyoyi a kasar, suna masu fatan gaggauta dawo da amfani da kundin tsarin mulkin kasar. Kana sun bayyana cikakken goyon bayan su, ga kokarin shiga tsakani da sassan masu ruwa da tsaki na kasa da kasa da na shiyyoyi ke yi.

Kaza lika kwamitin tsaron ya yi maraba, da sanarwar da kungiyar AU ta fitar, mai kunshe da adawar ta ga kwace mulki, da jingine kundin tsarin mulkin Burkina Faso, tana fatan za a martaba wa’adin mika mulki bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasar.

Daga nan sai mambobin kwamitin tsaron MDDr suka nuna rashin jin dadin su, kasancewar mai yiwuwa, mawuyacin yanayin rashin daidaiton siyasa, da zamantakewa da tattalin arziki, su haifar da dama ga ‘yan ta’adda, ta tayar da hankali a kasar, don haka suka karfafa gwiwar sassan kasa da kasa, da su tallafa wajen shawo kan matsalar siyasa dake addabar kasar.  (Saminu Alhassan)