logo

HAUSA

Masu satar mai na haifarwa Najeriya babbar matsala

2022-10-08 16:05:16 CMG Hausa

 

Shugaban majalissar dattijan Najeriya Ahmad Lawan, ya nuna damuwa game da yadda masu satar albarkatun mai ke haifar da wagegen gibi, ga kudaden shigar kasar. Lawan wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a, cikin jawabin sa na maraba, yayin zaman karbar daftarin kasafin kudin Najeriyar na shekarar 2023, wanda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar, inda ya ce tattalin arzikin kasar na fuskantar babban kalubale daga masu satar albarkatun mai.

Babban dan majalissar dattijan ya ce, "Bisa kiyasi, Najeriya na yin asarar adadin danyen mai da ya kai tsakanin ganga 700,000 zuwa 900,000 a kullum, adadin da ya kai asarar kusan kaso 29 zuwa 35 bisa dari, na jimillar kudin shigar kasar a rubu’in farko na shekarar nan ta 2022."

Lawan ya ce lokaci ya yi, da gwamnati ta dauki tsauraran matakai na dakile wannan mummunan laifi, duba da cewa, rashin yin hakan zai ci gaba da yin tarnaki ga kokarin da ake yi, na samar da muhimman ababen more rayuwa da fadada tattalin arzikin kasar.

Ya ce, "A gani na satar mai na cikin laifuka mafi muni a fannin gurgunta tattalin arziki. Barayin mai sun daura yaki da Najeriya da al’ummun ta, ta ayyukan su ke haifar da koma baya a bangaren fadada hanyoyin bunkasa kasa, da suka hada da raya fannin noma, da masana’antu, da hakar ma’adanai da dai sauran su.  (Saminu Alhassan)