logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Mika Dakin Adana Magunguna Na Zamani Ga Zimbabwe

2022-10-07 16:54:24 CMG Hausa

Kasar Sin ta mika wani dakin adana magunguna na zamani da darajarta ta kai miliyoyin daloli ga gwamnatin kasar Zimbabwe, domin bunkasa karfin kasar na adana magunguna da inganta tsarin bayar da kiwon lafiya.

Dakin adana magungunan, wanda kasar Sin ta gina tare da samar da kudin aikin, ya lakume dalar Amurka miliyan 22, kuma an yi masa mazauni ne a asibitin Sally Mugabe dake birnin Harare, wanda shi ne asibiti mafi girma na biyu a kasar.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwa da mika dakin, shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya yabawa kasar Sin bisa taimakon da take ba kasar a bangaren lafiya.

Ya kara da cewa, irin wannan goyon baya da tallafi, na nuna karfin alakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa kasarsa na godiya ga Sin, kuma sabon dakin adana magunguna ya kai matsayin inganci na kasa da kasa.

Harabar dakin ajiyar wadda daya ne daga cikin mafi girma a kudancin Afrika, ta kai murabba’in mita kimanin 43,000, sannan fadin ginin ya kai murabba’in mita 13,700. An fasalta shi ta yadda zai iya daukar kantoci 10,000 daga 6,000 da ake da shi yanzu haka.

A cewar shugaba Mnangagwa, karin zai taka muhimmiyar rawa wajen kara ingancin samun magunguna a tsarin kiwon lafiya na kasar da kuma kara inganta kokarin samar da kiwon lafiya ga kowa. (Fa’iza Mustapha)