logo

HAUSA

Firaministan Habasha Ya Kaddamar Da Dakin Adana Kayan Kimiyya Da Fasaha Da Kasar Sin Ta Samar

2022-10-06 16:39:19 CMG Hausa

Firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed, ya kaddamar da wani katafaren gidan adana kayan kimiyya da fasaha da kasar Sin ta samar, a Addis Ababa, babban birnin kasar.

Gidan adana kayan kimiyya da fasaha na Afirka mai shiffar Kubba, ya zama wani dandali da za a iya tunani a kuma kirkiro sabbin fasahohi na kimiyya, don tallafawa ci gaban kasar Habasha. Yana mai cewa, gidan zai taka muhimmiyar rawa wajen canja kasar Habasha zuwa tsarin tattalin arziki na zamani.

A wani bangare na bikin kaddamar da gidan, kasar dake gabashin Afirka, ta kuma karbi bakuncin taron kwaikwayon tunanin dan Adam na Afirka irinsa na farko.

Taron ya hallara masu bincike a bangaren kwaikwayon tunanin dan Adam, da masana kimiyyar lissafi da injiniyoyi, da ‘yan kasuwa da sauransu, domin tattauna dabarun da kasashen ke da su game da samun ci gaba mai dorewa, ta hanyar amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, ta hanyar musayar kwararru a fannin ilimi da aikace-aikace a sassa masu tarin yawa, kamar aikin gona, kiwon lafiya, harkokin kudi, bangaren samar da hidima, tsarin bayanai na yanki, da tsaron intanet da masana’antun samar da kayayyaki.

Babban darektan cibiyar fasahar kwaikwayon tunain dan Adam ta kasar Habasha Worku Gachena, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kasar Sin ba kawai tana taimakawa kasar Habasha wajen samun irin wannan katafaren gidan adana kayan kimiyya da fasaha na zamani ba, har ma tana kara baiwa kwararrun kasar Habasha kwarin gwiwa game da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam.(Ibrahim)