logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 75 a arewacin Najeriya

2022-10-06 16:12:55 CMG Hausa

A kalla mutane 75 ne aka bayar da rahoton sun mutu, bayan barnar da ambaliyar ruwa ta haddasawa al’ummomi 255 a jihar Yobe dake yankin arewacin Najeriya, kamar yadda wani jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa a yankin ya sanar a jiya Laraba.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe Mohammed Goje, ya shaidawa manema labarai a Damaturu, fadar mulkin jihar cewa, an samu rahoton mutuwar mutanen ne, tun a farkon damina a watan Mayu,sakamakon guguwar dake tafe da iska mai karfi da ambaliyar ruwa a jihar.

Goje ya bayyana cewa, adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu, sun hada da mutane 11 da suka mutu a sanadiyar hadarin kwale-kwale guda biyu. Sama da mutane 200 kuma sun samu raunuka daga bala’o’in da suka faru.

A cewar jami’in, ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, sama da gidaje dubu 31 ne ambaliyar ta shafa a cikin al’ummomi 255 daga kananan hukumomi 17 na jihar. Yana mai cewa, wadanda ke yankunan da ake fama da ambaliyar ruwan da kuma bakin magudanar ruwa ne suka fi fuskantar bala’in.

A cewarsa, an samu karin rayukan dake cikin hadari a fadin wasu kananan hukumomi 10 na jihar, yayin da ake ci gaba da sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar. (Ibrahim)