logo

HAUSA

Lawal Saleh: Muna fatan kara habaka hadin-gwiwa tsakanin Sin da Najeriya

2022-10-04 14:32:23 CMG Hausa

Ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 73, da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, kana, rana ce ta cika shekaru 62 da Najeriya ta samu ‘yanci daga turawan mulkin mallaka.

A yayin da kasashen biyu ke murnar ranar tare, wakilinmu Murtala Zhang ya samu damar zantawa da malam Lawal Saleh, wani shahararren mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, kana masanin harkokin kasashen waje a tarayyar Najeriya, inda ya yi fashin baki kan wasu manyan nasarorin da aka samu, a fannin inganta hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da tarayyar Najeriya, musamman a fannin samar da muhimman ababen more rayuwar al’umma.

Bugu da kari, ya bayyana fatansa ga makomar dangantakar kasashen Sin da Najeriya. (Murtala Zhang)