logo

HAUSA

Shugaba Xi Ya Bukaci Masu Aikin Nazarin Albarkatun Karkashin Kasa Da Su Kara Zamar Hako Karin Ma’adanai

2022-10-04 20:20:47 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci masu aikin nazarin albarkatun karkashin kasa dake aiki a lardin Shandong na gabashin kasar, da su ci gaba da kyakkyawan aikin da suke yi, tare da taka rawar gani a aikin hako karin ma’adanai.

Shugaba Xi ya yi wannan kira ne a ranar Lahadi, cikin wata wasika da ya aike ga tawagar ma’aikatan hukumar nazarin albarkatun karkashin kasa da albarkatun ma’adanai ta lardin Shandong.  (Saminu Alhassan)