logo

HAUSA

NDLEA a tarayyar Najeriya ta cafke tarin muggan kwayoyi a Lagos

2022-10-04 16:04:09 CMG Hausa

 

Hukumar dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ko NDLEA a takaice, ta ce ta yi nasarar cafke wani babban mai safarar kwayoyi, tare da gano tarin muggan kwayoyi da suka hada da tramadol, a wani gida dake unguwar Lekki na jihar Lagos dake kudancin kasar.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi, ya ce darajar kwayoyin da aka gano a ranar Juma’ar karshen makon jiya, ta kai sama da naira biliyan 8.8, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 20. Babafemi ya kara da cewa, da ma can NDLEA ta jima tana neman babban mai fasa-kwaurin kwayoyin tramadol zuwa Najeriya ruwa a jallo, amma sai a wannan lokaci ne suka yi nasarar cafke shi.

Tun a shekarar 2018 ne gwamnatin Najeriya ta sanya kwayar tramadol a cikin magungunan da aka hana sayar da su a matsayin maganin kashe radadin ciwo, muddin ba likita ne ya yi umarni ba. To sai kuma ana ci gaba da yin fasa-kwaurin kwayar tare da shan ta a matsayin kayan maye musamman tsakanin matasa.     (Saminu Alhassan)