logo

HAUSA

Shawarar BRI Na Ingiza Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya, In Ji Wani Kwararre

2022-10-04 16:14:16 CMG Hausa

Masani game da harkokin da suka shafi nahiyar Asiya, kuma mataimakin babban editan jaridar Al-Ahram ta kasar Masar Tarek el-Sonoty, ya jinjinawa manufofin da kasar Sin ke gabatarwa a shekarun baya-bayan nan, musamman ma shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, wadda ya ce tana da muhimmancin gaske, a fannin bunkasa ci gaban tattalin arziki da bunkasar duniya baki daya.

Tarek el-Sonoty, ya ce ta hanyar samar da ababen more rayuwa, da hadin gwiwar cimma moriyar juna tsakanin sassan kasa da kasa, Sin na ingiza samar da ci gaban bai daya, da bunkasa cudanyar ta da daidaikun kasashe, da ma sassan kasashen duniya baki daya.

Masanin ya ce Sin na da moriyar bai daya tare da kasashe masu tasowa, tana kuma fatan bunkasa hadin gwiwa da dukkanin kasashe masu tasowar, kuma manufofin kasar kamar shawarar ziri daya da hanya daya, na yin la’akari da yanayin kasashe masu tasowa.

Tarek el-Sonoty ya kara da cewa, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, an aiwatar da manyan ababen more rayuwa da dama, ciki har da wadanda aka aiwatar a Masar. Ya ce kamfanonin kasar Sin na gudanar da manyan ayyuka a Masar, ciki har da ginin sabon birnin gudanar da ayyukan hukuma a gabashin birnin Alkahira, da sabon birnin Alamein a arewa maso yammacin Masar.  (Saminu Alhassan)