logo

HAUSA

Shugaban kasar Mauritius ya yi imani da samun kyakkyawar makomar raya dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin

2022-10-03 16:05:47 CMG Hausa

Shugaban kasar Mauritius Prithvirajsing Roopun ya yi imani a kwanakin baya cewa, yayin da ake cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Mauritius da Sin, za a samu kyakkyawar makoma game da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Roopun ya bayyana hakan yayin da yake halartar liyafar murnar ranar cika shekaru 73 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin a ofishin jakadancin Sin dake kasar Mauritius a Port Louis, babban birnin kasar. Kana firaministan kasar Mauritius Pravind Kumar Jugnauth wanda shi ma ya halarci liyafar ya bayyana cewa, kasarsa abokiyar kasar Sin ce, yana fatan kasashen biyu za su kara yin mu’amala da juna da kuma zurfafa hadin gwiwarsu.

Jakadan Sin dake kasar Mauritius Zhu Liying ya jaddada a cikin jawabinsa cewa, shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Mauritius. Sin tana dora muhimmanci sosai ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kana tana fatan kara amincewar juna kan harkokin siyasa tare da kasar Mauritius, da kara yin mu’amala kan manyan tsare-tsare, da zurfafa hadin gwiwarsu a kokarin raya kyakkyawar makomarsu tare. (Zainab)