logo

HAUSA

ECOWAS ta bukaci al’ummar Burkina Faso da su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin tattaunawa

2022-10-03 16:04:41 CMG Hausa

 

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ko ECOWAS a takaice, ta bukaci al’ummar kasar Burkina Faso, da su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin tattaunawa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban kungiyar na yanzu, kana shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, ya kuma yi kira ga mahukuntan kasar Burkina Faso, da su mutunta alkawarin da suka yi tare da kungiyar ta ECOWAS.

Embalo ya sanar da cewa, za a tura tawagar kungiyar zuwa kasar, a wani bangare na kudirin ECOWAS na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Burkina Faso.

A daren ranar Jumma’a ne, Kyaftin Ibrahim Traore ya sanar da hambarar da shugaba Paul-Henri Sandaogo Damiba.

Wata sanarwa da shugabannin addinai da na al’ummar kasar suka fitar, ta bayyana cewa, Damiba ya amince ya sauka daga kan mulki a jiya Lahadi, domin kaucewa fuskantar mummunan abin da zai biyo baya.(Ibrahim)