logo

HAUSA

Yunkurin Amurka Da Birtaniya Da Australiya Na Yin Hadin Gwiwa Kan Jirgin Karkashin Ruwa Mai Amfani Da Makamashin Nukiliya Ya Ci Tura

2022-10-03 15:57:36 CMG Hausa

Yayin da wakilin kasar Sin ya ambato yadda aka tattauna batun hadin gwiwa a tsakanin kasashen Amurka da Birtaniya da Australiya kan jirgin  karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya a yayin babban taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA karo na 66, ya nuna cewa, an tabka muhawara mai zafi kan wasu muhimman fannoni. A karshe dai an ki amincewa da daftarin dokar da suka gabatar na neman halasta batun hadin gwiwarsu kan jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya.

Wasu al’ummomin kasashen yammacin duniya sun sha ambaton yadda ake bin doka da odar kasa da kasa, inda aka mayar da ka’idoji a matsayin harsashi. Amma abun da suka yi ya saba wa abin da suka furta. Hadin gwiwar da ke tsakanin Amurka da Birtaniya da Australiya kan jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, ta saba wa manyan yarjejeniyoyin kasa da kasa guda 3 a lokaci guda, wato yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya wato NPT, da yarjejeniyar ka’idojin hukumar IAEA, da kuma yarjejeniyar tabbatar da rashin kasancewar nukiliya a yankin kudancin tekun Pacific.

Salibi da haka ne a yayin babban taron IAEA karo na 66, sakamakon kokarin da kasar Sin da sauran kasashe mambobin hukumar suka yi, ya sa yunkurin kasashen 3 ya ci tura, lamarin da ya nuna cewa, masu adalci a duniya sun samu nasara, kana ana mutunta da kiyaye ka’idoji da yarjejeniyoyin kasa da kasa, sa’an nan, Amurka ta sake yin rashin nasara a yunkurinta na yin danniya. (Tasallah Yuan)