logo

HAUSA

Shugaban Najeriya ya lashi takwabin ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa

2022-10-02 16:27:00 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya jaddada fa’idar ci gaba da yaki da cin hanci da karbar rashawa da kuma hana damar aikata wannan matsala ta cin hanci da karbar rashawa a kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne, a yayin da yake jawabi ga al’ummar kasar da aka watsa, a wani bangare na shagulgulan bikin cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai, da aka gudanar jiya Asabar a Abuja, babban birnin kasar.

A game da nasarorin da aka samu a yaki da cin hanci a lokacin mulkinsa kuwa, Shugaba Buhari ya bayyana cewa, ci gaban da aka samu, wani mataki na gyaren-gyaren da ake yi, inda ya lashi takwabin ci gaba da aiwatarwa.

Ya ce, gwamnatinsa ta karfafa cibiyoyin yaki da cin hanci da karbar rashawa da samun tallafi daga kasashen duniya, wadanda suka taimaka wajen dawo da makuden kudade da ajiye ba bisa ka’ida ba a wajen kasar.

A cewarsa, ana ci gaba da samun karin wadanda ake hukuntawa da wannan laifi, tare da mayar da makuden kudaden da aka sace. (Ibrahim)