logo

HAUSA

Ya kamata a koyi fasahohin raya demokuradiyya na Sin

2022-10-02 16:53:46 CMG Hausa

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jama’ar kasar Kamaru Theodore Datouo ya bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kwanakin baya cewa, demukuradiyya ta sha bamban da yanayin kasa da kasa, tsarin demokuradiyya na gurguzu na kasar Sin ya dace da yanayin kasar Sin, kana ya taimaka wajen samun ci gaba a kasar, don haka ya kamata a yi koyi da fasahohin kasar Sin a wannan fanni.

Datouo ya ce, akwai bambancin al’adu a tsakanin kasa da kasa, don haka demokuradiyya ma ta sha bamban, ya kamata kowace kasa ta raya demokuradiyya bisa yanayinta.

Datouo ya kara da cewa, yadda ake aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tafarkin demokuradiyya na kasar Sin ya burge shi sosai, ta hanyar amfani da tsari mai dacewa, ana iya daidaita ayyukan yin zabe bisa demokuradiyya, da yin shawarwari, da ba da shawara, da sarrafa harkoki, da kuma sa ido. Sin ta samu mutane da dama tare da yankuna masu fadi, tsarin demokuradiyya yana baiwa jama’ar kasa, damar ba da shawara kan yadda za a tafiyar da harkokin kasa.

Hakazalika, ya ce, muddin raya tsarin tafiyar da harkokin kasa zai taimaka wajen samun ci gaba a kasa da kawo moriya ga jama’ar kasar. A matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma, Sin ta samu ci gaba cikin sauri, da samun nasarori a fannoni daban daban, kuma tsarin demokuradiyya na kasar Sin ne ya taimaka ga samun bunkasuwar kasar. (Zainab)