logo

HAUSA

WHO: An samu karuwar 63% na cututtukan da ke yaduwa daga dabbobi zuwa mutane a Afirka a cikin shekaru goma da suka gabata

2022-10-02 17:24:22 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi gargadi a kwanakin baya cewa, nahiyar Afirka na fuskantar barazanar barkewar kwayoyin cututtuka da ake dauka daga namun daji zuwa ga mutane, kamar kwayar cutar kyandar biri, wadda ta samo asali daga dabbobi, sannan ta sauya kama ta kuma kama mutane. Inda ta ce, an samu karuwar kashi 63 cikin 100 na barkewar kwayoyin cuta dake yaduwa tsakanin dabbobi zuwa mutane a yankin, daga shekarar 2012 zuwa 2022, idan aka kwatanta da makamancin lokacin daga shekarar 2001 zuwa 2011.

A cewar wata sanarwa da ofishin yankin Afirka na WHO ya fitar ta yi bayanin cewa, wani sabon bincike da hukumar ta gudanar ya ba da rahoton al'amuran kiwon lafiyar jama'a 1,843 da aka tabbatar a yankin Afirka, tun daga shekara ta 2001, kuma kashi 30 cikin 100 na wannan matsala, suna da nasaba da barkewar cututtukan da ake dauka daga namun daji zuwa mutane, musamman masu alaka da cutar Ebola, da zazzabin Dengue, da Anthrax, da annobar Plague, cutar kyandar biri da sauran ire-iren cututtuka.

Bisa la’akari da karuwar bullar cutar kyandar biri a baya-bayan nan, tun daga farkon bana, kasashe da yankuna 75 sun gabatar wa hukumar rahotanni kan yadda mutane fiye da dubu 16 suka kamu da cutar, ciki had da wasu 5 sun mutu, wadanda dukkansu suka fito daga kasashen Afirka.

Hukumar WHO ta yi gargadin cewa, karuwar yawan jama'a a nahiyar Afirka, tana haifar da bunkasar birane da kuma kutse ga muhallin namun daji, wanda ke kara hadarin barkewar cututtukan da jama’a ke dauka daga dabbobi, daga yankuna marasa ci gaba dake da karancin mazauna zuwa manyan birane.

Darektar WHO mai kula da ofishin yankin Afirka Matshidiso Moeti ta bayyana cewa, duk da ingancin harkar sufuri a Afirka, ana samun karuwar barazanar cututtukan da jama’a ke dauka daga dabbobi da ke kara shiga manyan birane. Don haka ta ce, tilas ne mu dauki mataki ba tare da bata lokaci ba, don magance wadannan cututtuka, kafin su yadu da hana Afirka zama wuri na kamuwa da cututtuka.

Dakile yaduwar irin wadannan cututtuka a Afirka yana da sarkakiya, kuma WHO ta ba da shawarar amfani da tsarin kiwon lafiya na bai daya, wanda ke bukatar sassa da dama, da fannonin ilmi, da al'ummomi domin yin aiki tare. Wannan ya kunshi masana, ciki har da wadanda ke aiki a fannin lafiyar bil-Adam, da dabbobi, da muhalli. Haka kuma ya kamata a raba bayanan sa ido na yau da kullum game da cututtuka da ayyukan mayar da martani, ga lafiyar dabbobi da na dan Adam a tsakanin masana cututtuka da sauran masana kiwon lafiyar jama'a.

Moeti ta ce, "Muna bukatar gudummawar kowa da kowa, don kandagarki da dakile yaduwar cututtukan dake yaduwa daga dabobbi zuwa ga mutane kamar Ebola, da cutar kyandar biri, da dai sauransu." Tana mai cewa, bazuwar cututtuka daga namun daji zuwa mutane, tana faruwa daga abubuwan da suka faru daga dabbobi zuwa mutane. Don haka ta ce, sai mun kawo karshen matsalolin dake tsakanin wadannan bangarori, kafin mu iya magance duk wani bangare na matakin da za a dauka.

Tun daga shekara ta 2008, WHO ta inganta hadin gwiwa da hukumar abinci da aikin noma ta MDD, da hukumar kula da lafiyar dabbobi ta duniya, don taimakawa kokarin da ake yi na magance barkewar cututtuka daga dabbobi zuwa mutane a fadin Afirka.

A kwanakin nan, hukumomin uku sun yi aiki tare yayin da cutar Ebola ta barke a karo na 14, wadda aka ga bayan ta a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ba da dadewa ba. (Ibrahim Yaya)