logo

HAUSA

Guterres ya nuna damuwa kan juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso

2022-10-02 16:14:36 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana damuwa kan halin da ake ciki a kasar Burkina Faso, bayan juyin mulkin da ya kai ga hambarar da shugaba Paul-Henri Sandaogo Damiba.

Stephane Dujarric, mai magana da yawun Guterres, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, babban sakataren ya yi Allah wadai da duk wani yunkuri na kwace mulki da karfin makamai, yana mai kira ga dukkan sassa masu ruwa da tsaki, da su kaucewa haddasa tashe-tashen hankula, maimakon haka su koma ga yin tattaunawa.

Sanarwar ta kara da cewa, Guterres ya bayyana cikakken goyon bayansa ga kokarin da yankin ke yi na dawo da kundin tsarin mulki cikin gaggawa. Kasar Burkina Faso na bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali da hadin kai, don yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuffuka a sassan kasar.

Haka kuma Guterres, ya nanata aniyar MDD, ta goyon bayan jama’ar kasar Burkina Faso, a kokarinsu na tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Juyin mulkin na ranar Jumma’a, shi ne na biyu a wannan shekara a kasar. Na farko a ranar 24 ga watan Janairu, wanda aka hambarar da shugaba Roch Kabore, daga baya Damiba ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasa a ranar 16 ga watan Fabrairu. A ranar Jumma’a da dare ne dai, Kyaftin Ibrahim Traore ya sanar da hambarar da shugaba Damiba.(Ibrahim)