Kasashen tsibiran tekun Pasifik sun fi bukatar sahihiyar gudummawa daga kasar Amurka
2022-10-01 16:53:18 CMG Hausa
Daga ranar 28 zuwa 29 ga watan Satumba, an gudanar da taron koli na kasar Amurka da kasashen tsibiran tekun Pasifik karo na farko a birnin Washington, inda shugaban kasar Amurka Joseph Biden ya bayyana cewa, makasudin gudanar da taron kolin shi ne, zurfafa dangantakar dake tsakanin Amurka da kasashen tsibiran tekun Pasifik. Kana ya sanar da samar da gudummawar da darajarsa ta kai dalar Amurka miliyan 810 ga kasashen tsibiran tekun Pasifik don inganta hadin gwiwarsu a fannonin tinkarar sauyin yanayi, da tattalin arzikin teku da sauransu.
Kafofin watsa labaru na kasar Jamus sun ruwaito cewa, gwamnatin kasar Amurka ta samarwa shugabannin kasashen tsibiran tekun Pasifik damar halartar taron da kuma gudummawar kudin dala, don hana Sin yin babban tasiri a yankin tekun Pasifik.
Abu ne mai kyau Amurka ta samar da gudummawa ga kasashen tsibiran tekun Pasifik, amma kasashen tsibiran tekun Pasifik ba sa bukatar alkawarin fatar baki, kuma ba sa son zama wani bangaren da ake amfani da shi don hana ci gaban kasar Sin, kuma sun fi bukatar sahihiyar gudummawa bisa yanayinsu na samun ci gaba.
Idan kasar Amurka tana son taimakawa kasashen tsibiran tekun Pasifik, ya kamata ta yi ayyuka hudu, wato samar da hakikanin gudummawa bisa alkawarin da ta yi, da daukar alhakin dake wuyanta game da tinkarar sauyin yanayi, da daukar matakai wajen kare yanayin hallitun teku, da kuma girmama kasashen na tsibiran tekun Pasifik, a maimakon maida su matsayin wani bangaren da ake amfani da shi a harkokin siyasa. (Zainab)