logo

HAUSA

Sojoji sun sanar da juyin mulki a kasar Burkina Faso

2022-10-01 16:28:44 CMG Hausa

 

Kaftan na sojojin kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore ya sanar da hambarar da shugaban kasar Lt. Col Paul-Henri Sandaogo Damiba, da yammacin jiya Juma’a.

A yayin wata sanarwa da aka watsa kai tsaye a kasar, Ibrahim Traore da ya jagoranci wata tawagar soji, ya sanar rushe kundin tsarin mulkin kasar da na rikon mulki da rushe gwamnatin rikon kasar tare da ayyana dokar hana fita daga 9 na dare zuwa 5 na asuba.

Ya kuma sanar da rufe iyakokin kasar har sai baba-ta-gani, da dakatar da duk wasu ayyukan jam’iyyun siyasa da na kungiyoyin al’umma.

Har ila yau, ya ce dukkan bangarori masu ruwa da tsaki za su hadu domin gabatar da sabon kundin tsarin mulki tare da nada shugaban kasar, ko na soji ko farar hula.

An jiyo karar harbe-harbe a Ouagadougou, babban birnin kasar Burkina Faso da safiyar jiya Juma’a, kana sojoji sun toshe hanyar zuwa fadar shugaban kasa da gidan talabijin na kasar da wasu muhimman wurare na birnin.

Jim kadan bayan nan ne kuma, fadar shugaban kasar Burkina Faso ta fitar da sanarwa tana kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu, inda ta ce ana tattaunawa domin dawo da kwanciyar hankali a kasar. (Fa’iza Mustapha)