logo

HAUSA

Majalisar Gudanarwar Sin Ta Gudanar Da Liyafa Domin Murnar Ranar Kafuwar Kasar

2022-10-01 16:02:07 CMG Hausa

Majalisar gudanarwar kasar Sin ta gudanar da liyafa a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing a jiya, domin murnar cika shekaru 73 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin dake gudana a ranar 1 ga watan Oktoba.

Da yake jawabi ga taron liyafar, firaministan Sin Li Keqiang, ya ce JKS za ta gudanar da babban taron wakilanta karo na 20 a bana, yana mai jaddada muhimmancin taron.

A cewarsa, tabbatar da kyakkyawan tubalin tattalin arziki na da matukar muhimanci ga dorewar ci gaban tattalin arzikin kasar. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta dauki managartan matakai na saukaka radadin kalubalen da ba a yi tsammani ba tare da aiwatar da manufofin da suka dace a kan lokaci, domin daidaita tattalin arzikin. Yana mai cewa, suna da kwarin gwiwa da karfin tabbatar da daidaituwar manyan alkaluman tattalin arzikin bisa matakin da ya dace.

Ya ce bisa manufar bude kofa ga waje da yin gyare-gyare a gida, kasar ta samu nasarori a fannin yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki irin na gurguzu, da kara bude kofa da karfafa cinikayya da zuba jari da kasashen waje da zurfafa hadin gwiwar kasuwanci tsakanin kasa da kasa, domin kasar Sin ta ci gaba da kasancewa wuri mafi dacewa na zuba jari da samun ci gaba irin na moriyar juna. (Fa’iza Mustapha)