logo

HAUSA

Wu Lei ya shiga jerin ‘yan kwallon dake takarar “Tafin Kafar Zinari na 2022”

2022-10-01 16:28:21 CMG Hausa

Dan kwallon kafar kasar Sin Wu Lei, ya shiga jerin ‘yan kwallon dake takarar “Tafin Kafar Zinari na 2022”. A bana za a ba da lambar a karo na 20, kuma za a zabi dan kwallo mafi kwarewa cikin shahararrun ‘yan kwallo 30 na kasashen duniya da dama, ciki har da Lionel Messi, da Karim Benzema da Neymar, da Robert Lewandowski, kamar dai yadda mashirya ba da lambar yabon suka bayyana a ranar 18 ga Satumbar nan.

“Tafin Kafar Zinari na 2022”, karramawa ce da Sarkin masarautar Monaco ke bayarwa tun daga shekarar 2003, da nufin martaba ‘yan kwallon kafa mafiya cimma manyan nasarori a sana’ar su. A shekarar bara, dan wasan kasar Masar Mohamed Salah ne ya lashe wannan lambar karramawar.

Bayan ga Wu Lei, akwai karin ‘yan kwallon Asiya da suka hada da Lee Chung-yong, da Son Heung-min daga Koriya ta kudu.

Wu daga kasar Sin na da shekaru 31, kuma a shekarar 2021 ya dawo buga kwallo a gasar zakarun kasar Sin mai lakabin “Shanghai Port” bayan ya taka leda a kungiyar Espanyol.

A ka’idar bayar da wannan lambar yabo, dukkanin masu sha’awar kwallon kafa za su iya kada kuri’ar su a shafin yanar gizo na mashirya ba da lambar, ta yadda za a kai ga zabar ‘yan wasa 10 na farko, a jerin wadanda aka zaba tun da farko.


Bierhoff: Gasar cin kofin kwallon kafa na 2022 babbar dama ce ga kasar Jamus


Babban manajan kungiyar kwallon kafar kasar Jamus Oliver Bierhoff, ya ce gasar cin kofin kwallon kafar duniya dake tafe a watan Nuwambar shekarar nan a Qatar, wata dama ce ga Jamus ta kashe kishirwarta, ta sake lashe kofin mafi daraja a kwallon kafar duniya. Oliver Bierhoff mai shekaru 54, kuma tsohon dan wasan kungiyar kwallo ta Jamus ya bayyana cewa, kungiyar su ta shirya tsaf, musamman ganin irin sauye sauye da duniya ke fuskanta ta fuskar samun karin sabbin dabarun inganta wasan, da kayayyakin horo, da na kula da lafiya da ake da su.

Bierhoff ya ce ko shakka ba bu, Jamus za ta iya lashe kofin na duniya na 2022, kamar yadda suka lashe kofin na 2014. Jami’in wanda a baya ya bugawa kungiyar Milan ta Italiya kwallo, na cike da kwarin gwiwar cewa, Jamus din za ta lashe gasar ta karshen shekara.

Bierhoff ya tabo tarihi, game da rashin nasarar da Jamus ta fuskanta a shekarar 2018 a Rasha, lokacin da aka fitar da Jamus daga gasar cin kofin na duniya tun a wasan rukuni.

Ya ce "Ba wanda zai manta da wannan lokaci na bakin ciki" Amma a wannan karo a cewar sa, Jamus ta shirya, za ta kai ga cimma wannan buri ba tare da wata matsala ba. Babban burin Jamus shi ne lashe wannan kofi da muke dauka a matsayin wata babbar dama, ta kara haskaka matsayin kungiyar kwallon kafar kasar".

A baya bayan nan, Jamus ta lashe wasanni 13 ba tare da an yi nasara a kan ta ba, a gasar kulaflikan kasashe, wanda hakan tamkar share fage ne na tunkarar gasar cin kofin na duniya dake tafe a Qatar.

Domin cimma burin ta, kungiyar Jamus ta shirya tafiya kasar Oman a ranar 14 ga watan Nuwamba dake tafe, domin buga wasan sada zumunta da Oman. Game da hakan, Bierhoff ya ce "Wannan wata dama ce, ta sabawa da yanayin yankin da za a buga gasar ta cin kofin duniyar cikin sauri. Kaza lika kungiyar ta Jamus karkashin kocin ta Hansi Flick, za ta yi amfani da wannan dama wajen yin duk sauye sauye da suka rage, kafin bude gasar ta kasa da kasa". A cewar Bierhoff buga gasar duniya a tsakiyar kakar wasanni, na bukatar sabon salon wasa na musamman”.

Jami’in ya ce ba wata matsala da sabbin shirye shiryen da suke yi zai haifar. ‘Yan wasan za su hada wasannin su na kulaflika, da na shirin gasar cin kofin duniya tare. Su kuma jagororin kungiyar kasar za su sanya ido a bangaren lura da lafiyar ‘yan wasa, sakamakon karin wasannin da za su tunkara a wannan gaba.

Bierhoff ya ce ‘yan kwallon Jamus na fatan zuwan wannan babbar gasa ta kasa da kasa cike da nishadi.


Federer: Ba zan bace gaba daya daga fagen kwallon tennis ba!


Tauraron kwallon tennis na duniya Roger Federer, ya tabbatar da cewa, ko bayan ya bar buga gasar kasa da kasa ta tennis, zai ci gaba da shiga ana damawa da shi a wannan harka. Federer dan asalin kasar Switzerland, wanda a yanzu ke da shekaru 41, ya shaidawa magoya bayan sa a ranar 15 ga watan nan cewa, zai yi ritaya daga buga babbar gasar tennis ta Grand Slams, da gasar ATP Tour, daga gasar Laver Cup ta birnin London da aka kammala a wannan wata.

Kafin ritayarsa, Federer ya lashe gasar Grand Slam 20, ya kuma tabbatar da cewa, gasar Laver Cup ta birnin London ce gasar karshe da zai buga, amma kuma zai ci gaba da taka rawar gani a harkar tennis, ko da yake bai bayyana me zai yi bayan ritayar ba.

Federer ya ce "Ina so na bayyanawa magoya baya na cewa, ba zan bace gaba daya daga tennis ba. Wasa ne da ya ba ni manyan nasarori. Na jima a cikin sa sosai. Na shaku da abubuwa da dama a cikin sa. Ina fatan sake haduwa da ku baki daya. Don haka nake tabbatar muku cewa, za mu sake ganin juna. Sai dai har yanzu ban san ta wane yanayi, ko a yaushe za mu hadu din ba, har yanzu ina kara tunani a kan haka”.

Tauraruwar Federer ta fara haskawa tun a shekarar 1998 lokacin yana da shekaru 16 da haihuwa, kafin daga bisani ya lashe gasar Grand Slam ta farko a shekarar 2003 a Wimbledon. A matsayin sa na dan wasan tennis mafi samun daukaka a tarihi, Federer ya ce yana alfahari da tsawon zamani da ya kwashe yana haskawa a wasan tennis.

Ya ce "Na yi suna saboda kasancewa ta mai haskakawa sosai tun a farkon shiga ta wannan wasa. Ko kuma saboda na rika yin nasara ina kuma samun koma baya ne? Daga baya dai na ci gaba da samun nasarori ba kakkautawa, na kasance daya daga ‘yan wasa mafiya nasara a tarihin kwallon tennis, wanda ni kai na hakan ya rika bani mamaki. Hakan ya sa na samun matukar gamsuwa a zuciya ta".