logo

HAUSA

Hadin kan Sin da Argentina ya zamo abun misali ga kasashe maso tasowa

2022-09-30 10:33:36 CMG HAUSA

 

A bana ne ake cika shekaru 50 da kafuwa huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Argentina. A matsayin daya daga cikin wasu ayyukan murnar wannan muhimmin lokaci, kana shekarar sada zumunta tsakanin kasashen biyu na shekarar 2022, an gabatar da dandalin manyan shugabanni, na mu’amalar al’adu tsakanin kasashen biyu, inda shugabannin kasashen biyu suka aikewa juna wasikar taya murna. Abin da ya bayyana cewa, shugabannin kasashen biyu na dora babban muhimmanci kan hadin kansu.

A cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, dangantakar dake tsakaninsu ta sauya, daga abokai masu nisa da juna zuwa abokan hadin kai a dukkanin fannoni, matakin da ya amfani al’ummominsu, kuma ya shaida cewa, za a iya cimma moriya tare.

Mu’ammalar al’adu da cudanyar al’ummomin biyu, tushe ne na hadin kan Sin da Argentina a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata. Daga cikinsu kuma, hadin kan kafofin yada labarai na ba da muhimmanci matuka.

A gun dandalin manyan shugabanni na mu’amalar a’adu, kafar CMG ta kasar Sin, ta sanar da hadin kai da kafofin yada labarai na Argentina, don shirya “makon al’adun kasashen biyu”, da kafa “salon yada labaru da dumi-dumi tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka” da dai sauransu.

Sakantare mai kula da kafofin yada labarai na kasar Argentina Juan Ross ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yana mai cewa, Sin da Argentina sahihan abokan hadin gwiwa da aminai ne dake haifar da moriyar juna. (Amina Xu)