logo

HAUSA

Dakarun Somaliya sun hallaka mayakan al-Shabab 40 a yankin tsakiyar kasar

2022-09-30 10:40:01 CMG Hausa

Rundunar sojojin kasar Somaliya ko SNA a takaice, wadda ke samun goyon bayan mayakan sa kai na Ma'awisley, ta yi nasarar hallaka mayakan al-Shabab 40. Sojojin na Somaliya, sun yi nasarar fatattakar dakarun na Al-Sabab ne a jiya Alhamis a yankin Hiran dake tsakiyar kasar.

Kwandojin SNA sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Somaliya cewa, sojojin gwamnati sun yi dauki ba dadi da ’yan ta’addan ne a kauyen Ceel-Qooxle, kuma suna ci gaba da binciken gyauron mayakan da suka tsere bayan fafatawar.

Kauyen Ceel-Qooxle dai na cikin kauyuka da dama da sojojin gwamnati suka kwato, bayan ayyukan soji masu tsanani da ake aiwatarwa a yankunan kudanci da tsakiyar Somaliya, karkashin hadin gwiwar dakarun gwamnati da mayakan sa kai masu mara musu baya.

A baya bayan nan sojojin gwamnatin Somaliya sun matsa kaimin kakkabe gyauron mayakan kungiyar al-Shabab, inda suke korar su daga wuraren da suka kai kusan sama da shekaru 10 suna rike da su. (Saminu Alhassan)