logo

HAUSA

CMG ta gabatar da shirin bidiyo na ba da bayani kan bunkasuwar kasar Sin cikin shekaru 10 da suka gabata da harsuna da dama

2022-09-30 15:41:55 CMG HAUSA

 

Yau Juma’a 30 ga wata, an yi bikin gabatar da shirin bidiyo, na ba da bayani kan bunkasuwar kasar Sin a cikin shekaru 10 da suka gabata, da harsuna da dama wanda kafar CMG ta tsara. Mataimakin ministan hukumar yayata manufofin kasar Sin, kana shugaban CMG Shen Haixiong ya halarci bikin tare da aiwatar da wannan shiri tare da sauran mahalarta bikin.

A gun bikin, shugaban asusun Kuhn, Robert Lawrence Kuhn, da mataimakin darektan kungiyar masanan Sin da duniya David Blair, da dai sauran kwararru sun halarci bikin ta kafar bidiyo, tare da nuna kyakkyawan fatansu. Jami’an hukumomin dake da nasaba da aikin su ma sun halarci bikin.

An ba da labarin cewa, daga ranar 30 ga wata, za a fara watsa wannan shiri na bidiyo a kafofin harsunan Turanci, da Spaniyanci, da Faransanci da Larabci da na harshen Rasha wadanda suke hannun kafar CGTN.  (Amina Xu)