logo

HAUSA

Shugabannin kasar Sin sun ajiye furanni domin girmama jaruman kasar

2022-09-30 14:16:14 CMG HAUSA

 

Yau Juma’a 30 ga wata, rana ce ta tunawa da jaruman da suka sadaukar da rayukansu domin kasar Sin da jama’arta. Kuma da safiyar wannan rana, an gudanar da gaggarumin bikin ajiye furanni domin tunawa da girmama wadannan jarumai.

Shugabannin kasar Sin, ciki har da shugaba Xi Jinping, da wakilan bangarorin daban-daban sun halarci bikin, inda aka waiwayi ayyukan da ’yan mazan jiyan suka yi, tare da nuna musu mutunta da sunan kasar Sin.

A watan Agusta na shekarar 2014, aka ayyana ranar 30 ga watan Satumbar kowace shekara, a matsayin ranar tunawa da jaruman kasar, inda aka sanya hakan cikin dokar kasar Sin. A watan Afrilu na shekarar 2018 kuma, aka zartas da dokar “kare hakkin jaruman kasar Sin, wadanda suka sadaukar da rayukansu domin jamhuriyyar jama’ar kasar Sin”, inda aka tabbatar da cewa, ranar 30 ga watan Satumbar kowace shekara, rana ce ta jaruman kasar, kuma kasar ta gudanar da gaggarumin biki don tunawa, da mutunta wadannan jarumai a hasumiyar tunawa da su da aka gina a filin Tian’anmen dake tsakiyar birnin Beijing. (Amina Xu)