logo

HAUSA

EAC ta bukaci mambobinta da su inganta matakan kandagarki bayan barkewar Ebola a Uganda

2022-09-30 10:44:53 CMG Hausa

Sakatariyar kungiyar raya yankin gabashin Afirka ko EAC, ta yi kira ga kasashe mambobin kungiyar da su kasance cikin shirin ko ta kwana, da nufin aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba, bayan samun rahoton bullar cutar Ebola a kasar Uganda.

A ranar 20 ga watan Satumbar nan ne kasar Uganda, wadda daya ce daga kasashe 7 mambobin EAC, ta bayyana bullar Ebola, bayan samun wanda ke dauke da nau’in kwayoyin cutar na Sudan, a gundumar Mubende dake tsakiyar Uganda.

Cikin wata sanarwa da EACn ta fitar daga helkwatarta dake birnin Arusha na arewacin kasar Tanzania, ta bukaci kasashe mambobinta da su zurfafa sanya ido, da yin gwaje-gwaje a dakunan bincike, musamman ma a sassan kan iyaka.

Kaza lika EACn ta yi kira ga mambobinta da su aiwatar da matakan da suka dace, na kandagarki da shawo kan cutar, tare da fadada wayar da kan al’ummu game da cutar. (Saminu Alhassan)