logo

HAUSA

Har Kullum Kasar Sin Na Goyon Bayan Adalci Game Da Batun Falasdinawa

2022-09-29 16:34:00 CMG Hausa

Cikin tsawon lokaci, batun takaddamar yankuna tsakanin al’ummar Falasdinu da tsagin Yahudan Isra’ila na jan hankalin sassan kasa da kasa, musamman ganin yadda rashin warware batutuwa masu nasaba da mallakar yankuna tsakaninsu ke ta haifar da tashe-tashen hankula, masu kaiwa ga asarar rayuka.

Ko shakka babu, akasarin kasashen duniya na goyon bayan warware rikicin Falasdinu da Isra’ila, wanda ya samo asalin tun a tsakiyar karni na 20, ta hanyar kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu, wadanda za su zauna da juna lami lafiya. To sai dai tsawon shekaru ke nan, wannan bukata ta gaza cimma nasara, duba da yadda manyan sassan dake da ruwa da tsaki, musamman ma Amurka mai da karfin fada a ji, ke nuna goyon baya ga tsagin Isra’ila, da yin watsi da matakan komawa teburin sulhu, hakan ya sa Ira’ila ke fakewa da wannan dama, tana fadada mamayar yankunan Falasdinu ba bisa ka’ida ba.

Duk da haka, a bangaren kasashen dake ci gaba da goyon bayan adalci, da biyayya ga manufofin MDD masu nasaba da wannan batu, kasar Sin ta jima tana jaddada muhimmancin tabbatar da daidaito da adalci, da fatan a komawa gudanar da shawarwari domin kawo karshen wannan sa-in-sa.

Ko shakka babu, matsayar kasar Sin na kan turbar adalci, ita ce kuma ta yi daidai da ra’ayoyin mafi yawan kasashen duniya, na kawo karshen rashin zaman lafiya da ya jima yana addabar wannan yanki na gabas ta tsakiya.

Duba da cewa, wannan batu ne mai dadadden tarihi, wanda kuma kai tsaye warware shi ke da alaka da wasu muhimman sassan kasa da kasa, fatan duniya a yanzu shi ne gwamnatin Isra’ila, da kungiyar PLO ta ’yantar da Falasdinawa, da masu shiga tsakani da suka hada da MDD, da Amurka, da Rasha, da tarayyar Turai, da kungiyar kasashen Larabawa ta LA da sauransu, za su rungumi matsayar kasar Sin ba tare da bata lokaci ba, ta yadda za a kawo karshen wannan takaddama ta Falasdinu da Isra’ila cikin ruwan sanyi.(Saminu Alhassan)