logo

HAUSA

Shugabannin kasashen Sin da Japan sun taya juna murnar cika shekaru 50 da dawo da huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu

2022-09-29 14:12:30 CMG HAUSA

 

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Japan Fumio Kishida, suka aikawa juna sakon murnar cika shekaru 50 da maido da huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Xi Jinping ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, bangarorin biyu sun zurfafa hadin kansu a fannoni daban-daban, lamarin da ya amfanawa al’ummomin kasashen biyu, da ciyar da zaman lafiya da bunkasuwar shiyya-shiyya da ma duniya baki daya.

Ban da wanann kuma, Xi ya jaddada cewa, Sin na dora muhimmanci matuka kan bunkasuwar huldar kasashen biyu, yana mai fatan kara hada kai da Fumio Kishida, don inganta huldar dake tsakaninsu dake dacewa da halin da ake ciki a sabon zamani bisa zarafi mai kyau.

A nasa bangare, Fumio Kishida ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 50 da suka gabata, kasashen biyu sun samu ci gaba mai armashi a fannin tattalin arziki da al’adu da zirga-zirgar mutane a tsakaninsu. Yana mai cewa, bude wani sabon babin huldar dake tsakaninsu yana da ma’ana matuka.

Sannan firaministan kasar Sin Li Keqiang shi ma ya aika wa Fumio Kishida sakon murnar cika shekaru 50 da komar da huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Japan. (Amina Xu)