logo

HAUSA

An yi taron manema labarai kan ayyukan diplomasiyyar kasar Sin a sabon zamani

2022-09-29 16:03:09 CMG HAUSA

 

Da safiyar yau Alhamis ne aka kira taron manema labarai, kan ayyukan diplomasiyyar kasar Sin a sabon zamani a nan birnin Beijing, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Ma Zhaoxu, ya amsa tambayoyin da manema labarai suka gabatar masa, game da ayyukan diplomasiyyar kasar Sin a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Ma Zhaoxu ya nuna cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi hangen nesa game da makomar bil Adama da ya gabatarwa MDD, da dai sauran manyan taruka na ra’ayin da Sin take dauka, game da daidaita ayyukan duniya, wato nacewa ga manufar bude kofa da yin hakuri da juna, da tushen dokar kasa da kasa, da hadin kai da sulhuntawa, da gudanar da ayyuka bisa halin da ake ciki, ta yadda za a jagorancin tsarin daidaita harkokin duniya, da kwaskwarimar da za a yi kan tsarin kasa da kasa, don ba da tabbaci ga duniya, wadda yanzu ke cikin yanayi na rashin tabbas. (Amina Xu)