logo

HAUSA

Hukumar AUABC ta jaddada kira ga mambobin AU da su amince da yarjejeniyar yaki da cin hanci na Afrika

2022-09-29 11:37:54 CMG Hausa

Hukumar ba da shawara kan yaki da cin hanci ta kungiyar tarayyar Afrika AU, wadda aka fi sani da AUABC, ta ci gaba da yayata bukatar dukkanin kasashen Afirka, da su amince da yarjejeniyar bai daya ta yaki da cin hanci a dukkanin nahiyar.

An dai kafa hukumar ta AUABC ne a shekarar 2009, da nufin taimakawa Afirka, da dabarun shawo kan wannan mummunan laifi da ke mayar da hannun agogo baya.

Da take tsokaci game da bukatar, babbar sakatariyar hukumar mai mazauni a kasar Tanzania Charity Nchimunya, ta ce suna ci gaba da tattaunawa da sassa masu ruwa da tsaki na kunfiyar AU, domin fayyace musu muhimmancin amincewa da yarjejeniyar.

Charity Nchimunya, wadda ta bayyana hakan yayin zaman karin haske da manema labarai game da manufar, a birnin Nairobin kasar Kenya, ta ce tuni kasashen Afirka 48 suka sanya hannu kan yarjejeniyar, yayin da karin kasashen nahiyar 7 ke daf da amincewa da ita.

Kasashen 7 su ne Janhuriyar Afirka ta tsakiya, da Cape Verde, da Djibouti, da Eritrea, da Eswatini, da Somalia da kuma Sudan ta kudu.  

(Saminu Alhassan)