logo

HAUSA

Kasar Sin za ta gudanar da bikin gabatar da kwandon furanni ga jarumai gobe

2022-09-29 14:01:10 CMG Hausa

Ranar 30 ga watan Satumba, ita ce ranar tunawa da shahidan kasar Sin. Sabo da haka, gobe da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin JKS da jagororin kasar, da kuma wakilai daga sassa daban daban na rayuwa, za su gabatar da kwandunan furanni ga jarumai a filin Tiananmen dake cikin garin Beijing.