logo

HAUSA

Sin ta fitar da rahoton yin karatu a ketare na shekarar 2022

2022-09-29 10:46:32 CMG HAUSA

 

Kungiyar masana da kwararru, da babban bankin kasar Sin, da jami’ar koyon ilmin tattalin arziki da hada-hadar kudi ta kudu maso yammacin kasar Sin, sun yi hadin gwiwar gudanar da wani nazari, tare da gabatar da rahoton yin kararu a ketare na shekarar 2022 a jiya Laraba, rahoton ya nuna cewa, yawan daliban kasar Sin da suka yi karatu a ketare, na samun bunkasuwa a bangarori daban-daban, kuma karin daliban duniya da yawa sun amince da matakin karo ilimi a nan kasar Sin.

Rahoton ya ba da kididdigar cewa, a shekarar 2019, yawan daliban Sin da suka yi karatu a kasashen waje ya kai 1,061,511, adadin da ya kasance mafi yawa a duniya baki daya.

Ban da wannan kuma, rahoton ya nuna cewa, dalibai Sinawa da suka yi karatu a ketare, sun nuna himma da kwazo, wajen komawa gida don ba da gudunmawarsu a cikin harkokin kasar Sin.

Dadin dadawa, rahoton ya yi karin bayani kan daliban ketare, wadanda ke karo ilmi a nan kasar Sin. Ya ce, a cikin shekarar 2018, Sin ta kai matsayi na uku a duniya, kuma ta farko a Asiya, wajen jawo hankalin daliban kasashe daban-daban, wanda hakan ya sa karo ilmi a kasar Sin ya samu amincewa daga daliban ketare da dama.  (Amina Xu)