logo

HAUSA

An gudanar da taro kan "ci gaba mai inganci da nasarorin da aka samu a jihar Xinjiang" a taro na 51 na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD

2022-09-28 12:18:31 CMG Hausa

An gudanar da taron gefen kasar Sin kan "ci gaba mai inganci da nasarorin da aka samu a jihar Xinjiang" a taro karo na 51 na kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD a birnin Bole dake jihar Xinjiang ta kasar. Yayin taron da aka yi ta kafar bidiyo da kuma ido da ido a jiya, masana da malamai fiye da goma na gida da waje da wasu wakilan jama'ar jihar Xinjiang da wakilan daliban kasashen waje da ke karatu a kasar Sin, sun yi tattaunawa mai zurfi kan sauye-sauyen da aka samu a jihar Xinjiang sakamakon ci gaba mai inganci, da kuma nasarorin da aka samu a fannin kare hakkin bil'adama.

Hussein Ibrahim Morsy, shugaban kwalejin koyar da harsuna da fassara na jami'ar kimiyya da fasaha ta Masar, kuma farfesa a sashen koyar da Sinanci na jami'ar Ain Shams, yana ganin cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan aikin ba da ilmi ga kananan kabilu da yankunan da ‘yan kananan kabilu ke taruwa, kuma ta dauki kwararan matakai na kare hakkin kananan kabilu wajen samun ilimi, da kyautata halin yankunan da ‘yan kananan kabilu ke taruwa da jama’ar dake zaune a yankunan da inganta zaman rayuwar jama'a a yankunan, kuma an samu manyan nasarori.

Ye Suya, wata daliba ‘yar Najeriya dake karatu a jami'ar horar da malamai ta Zhejiang, da Ou Jingya, daliba ‘yar kasar Mozambique, sun ziyarci jihar Xinjiang a baya-bayan nan, kuma sun bayyana cewa, hadin kan al’ummar yankin da kokarin da gwamnatin ke yi na karewa da kuma gadon abubuwan tarihi na al’adu da ake gada daga kakanni kakanni, sun burge su kwarai da gaske. A ganinsu, Xinjiang "wuri ne mai cike da karfi".

Shi kuwa babban darektan cibiyar binciken hakkin dan Adam ta jami'ar koyon dokokin shari'a ta arewa maso yammacin kasar Sin, Chang An cewa ya yi, yadda Amurka da kasashen yammacin duniya ke yayata batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam a jihar Xinjiang, hakika, alama ce ta zahiri ta siyasantar da hakkin bil’adama da amfani da batun don cimma burinsu. Kana ya lalata albarkatun jama’ar kasa da kasa a fannin kare hakkin bil’adama don nuna danniya ko babakere, lamarin da ya sabawa manufar ci gaban kare hakkin bil'adama a duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)