logo

HAUSA

Yadda BRI da FOCAC suke taka rawa wajen bunkasa kasashen Sin da Najeriya

2022-09-28 10:01:20 CMG Hausa

A ranar 1 ga watan Oktoban bana, rana ce da kasar Sin ke murnar cika shekaru 73 da kafuwar Jamhuriyar Al’ummar Sin, yayin da Najeriya ke murnar cika shekaru 62 na samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallakar Burtaniya. Tun lokacin da kasashen Sin da Najeriya suka kulla huldar diflomasiya a tsakaninsu a ranar 10 ga watan Fabarairun shekarar 1971, dangantakar kasashen take ta kara bunkasa, har ma su fadada alakar zuwa fannoni daban-daban. Kafin kulla wannan alaka, jami’an kasashen biyu sun sha ziyartar kasashen juna a mabanbantan lokuta.

Najeriya dai ita ce, kasa mafi yawan al’umma da ma karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, yayin da kasar Sin ke zama babbar kasa mai tasowa mafi yawan al’umma kana ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Yanzu haka, kasashen Sin da Najeriya na alaka a fannonin aikin gona, da al’adu, ilimi, da kafofin watsa labarai, mata da matasa, harkokin cinikayya da sauransu.

Yayin da kasashen ke raya alaka a tsakaninsu, sun kuma yi alkawarin kare manufofi da muradun juna da rashin tsoma baki a harkokin cikin gidan juna da goyon bayan juna a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya da makamantansu.

Bugu da kari, sassan biyu sun lashi takwabin karfafa tuntubar juna don tabbatar da ganin an aiwatar da sakamakon da aka samu yayin taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka (FOCAC) da shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Shawarar “ziri daya da hanya daya” (RBI), shawara ce da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekarar 2013. Da farko shawarar ta mayar da hankali ne kan zuba jari a fannin ababan more rayuwa, da Ilimi, da gine-gine, da hanyoyin mota da layin dogo, da rukunin gidajen kwana, da tashoshin samar da wutar lantarki, da sauran muhimman fannoni da dan-Adam ke bukata。

Shawarar “ziri daya da hanya daya” ta magance gibin ababen more rayuwa, kana tana da karfin bunkasar tattalin arziki a yankin Asiya da Fasifik da yankunan tsakiya da gabashin Turai har ma da nahiyar Afirka. Masana sun yi imanin cewa, shawarar tana da muhimmanci wajen bunkasa alakar kasa da kasa. Kuma yanzu haka, akwai kasashe kimanin 140 da kungiyoyin kasa da kasa sama da 28 da suka sanya hannu kan shawarar, duk da yadda wasu kasashen yamma ke yi mata bahaguwar fahimta. A yayin da dandalin FOCAC ke zama wani dandali da kasashen biyu ke tattauna muhimman batutuwa dake shafar moriyarsu, da yadda Sin ke bijiro da wasu tsare-tsare da nufin taimakawa kasashen nahiyar Afirka, ciki har da Najeriya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)