logo

HAUSA

An Sake Tono Asirin Amurka

2022-09-28 21:58:13 CMG Hausa

Jami’ar Stanford ta kasar Amurka da wani kamfanin nazarin yanar gizo sun kaddamar da rahoton bincike a watan jiya cewa, cikin shekaru kusan 5 da suka gabata, Amurka ta baza labaran bogi ta hanyar amfani da shafukan kafafen sada zumunta da dama, wadanda suka yayata kalaman amincewa da kasashen yammacin duniya, da bata sunan kasashen Sin da Rasha da Iran da dai sauransu. rahoton ya yi nuni da cewa, mai yiwuwa ne rundunar Amurka ce take aika wannan danyen aiki. Yanzu kuma an rufe wadannan shafuka duka.

Har kullum Amurka ta kware wajen kirkiro labaran bogi, da kawar da hankulan al’umma daga gaskiya. Aikin da jami’ar Stanford da sauran hukumomi suka yin a bankado wannan barna a fili, wani bangare ne na yaki da baza labaran bogi a yanar gizo da Amurka take yi, wadda ke kulla makarkashiya a fannoni daban daban, alal misali, hambarar da gwamnatin kasashe,da rura wuta don samun riba ta hanyar kirkiro da baza labaran bogi, da dora wa wasu laifi, da shafa wa abokan gaba da ke adawa da tunaninta bakin fenti. Lalle Amurka da ta dade tana kirkiro karya da mayar da baki fari, kuma ba a gaskata ta ba. (Tasallah Yuan)